<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>214</hymn_number>
<title>Alherin Yesu, Ubangijina LW214</title>
<lyrics>[V1]
 1) Alherin Yesu, Ubangijina,
 Ya wuce gaban ganewa.
 Gama tun muna maƙiyansa fa,
 Ya mutu don mu sami rai.

[V2]
 KORUS
 Waɗanda suka karƃi Yesu
 Ya ba su iko su zama nasa.
 Ƴaƴa ne idan sun ba da
 Gaskiya ga sunansa.

[V3]
 2) Ban iya gane ko in fassara
 Abin da aka aika ba,
 Amma na sani cikin zuciyata
 Salama tana nan zaune.
 Korus

[V4]
 3) Ruhu Mai Tsarki yana aikinsa
 A cikin masu zunubi
 Domin su san bukatar zuciya,
 Su karƃi Yesu Mai Ceto.
 Korus

[V5]
 4) Ban san ran zuwan Ubangiji ba,
 Amma a shirye na ke fa
 In tarbe shi a cikin sarari,
 Ko kuwa in bi ta mutuwa.
 Korus</lyrics>
<author>McGranahan, James (1840-1907), Whittle, Daniel Webster (1840-1901), Nathan, Elias (1840-1901)</author>
</song>